1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya na kokarin kwato garuruwa 6 a Borno

December 31, 2018

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da rufe hanyar Maiduguri zuwa Munguno wanda ke hadewa da Baga saboda fafatawar da take yi da mayakan Boko Haram wanda su ka karbe iko da gauruwa 6 a kwanaki bakwai da su ka shude.

Nigeria Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo

 

Rahotanni sun tabatar da cewa mayakan Boko haram sun karbe iko da wasu biranen Baga da Doron Baga da Kekeno da Kukawa da Cross Kauwa da Bunduran a jihar Borno da ke shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya. Akwai bayanai da ke nuna cewa mayakan na kokarin fadada wuraren da suke iko da su inda suke fafatawa da Sojoji domin kwace garin Munguno da ke Arewacin jihar Borno.

Sai dai babban hafsa da ke kula da horarwa da ayyukan tabbatar da tsaro na rundunar Sojojin Manjo Janar Lamidi Adewosun ya tabbatar da cewa Baga ba ta hannun mayakan Boko Haram, inda ya ce " Sun dai yi kokarin kwaceta amma ba su samu nasarar hakan ba….”

Yaran 'yan gudun hijira na bukatar taimakon gaggawaHoto: DW

  Jama’ar yankin na ta ficewa daga garuruwan domin zuwa yanknan da suke ganin tudun na tsira ne. Wannan ya sa hukumomi daukar matakai na rufe hanyoyin mota da ke zuwa wadannan garuruwa, abin da ya rutsa da dubban jama’a maza da mata, manya da yara da ke kokarin ficewa daga yankunan saboda gudun zama karkashin ikon mayakan Boko Haram.   

Daruruwan ‘yan gudun hijira na isa Maiduguri a galabaice saboda wahalhalu da suka shiga wajen ficewa daga wadannan yankuna da ake gwabza fada tsakanin sojin Najeriya da ke neman kwato garuruwan da Boko Haram suka karba a ‘yan kwanakin nan.

Malama Hafsa wata tsohuwa ce da ta yi tafiyar kafa zuwa Maiduguri, ta ce " Da Boko Haram suka zo garinsu mamaye ko'ina suka yi, sshi ya sa muka gudu, mun yi tafiya da kafa mun iso Maiduguri da kyar cikin wahala. Yanzu haka kuma ba mu da komai, ba tabarma ba wurin zama ba abinci da za mu ci "

Kusan a iya cewa ana cikin halin rudani inda lamuran tsaro ke kara tabarbawa a wannan yankin wanda ya shafe shekaru kusan gona yana fama da rikicin Boko haram.