1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya sun kashe yan Boko Haram 50

Abdullahi Tanko Bala
October 23, 2025

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 50 wadanda suke amfani da jirage marasa matuka wajen kai hari kan barikokin soji a arewa maso gabashin kasar

Nigeria Damboa 2016 | Soldaten der nigerianischen Armee im Kampf gegen die Terrororganisation Boko Haram
Hoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Najeriya kasa mafi yawan jama'a a Afirka ta dade tana fama da 'yan kungiyar Boko Haram da na ISWAP a yammacin Afirka kusan shekaru 16 a kokarin da mayakan jihadin ke yi na kafa daula arewa maso gabashin kasar.

Da sanyin safiyar alhamis ne sojojin Najeriyar tare da rakiyar jiragen yaki suka far ma 'yan tada kayar bayan da suka kai hare hare a garuruwan Dikwa da Mafa da Gajibo a jihar Borno da kuma Katarko a jihar Yobe mai makwabtaka a cewar Leftanar kanar Sani Uba mai magana da yawun sojojin kamar yadda ya fada a cikin wata sanarwa.

Sai dai kuma sojojin basu fadi kungiyar da ta kai hare haren ba amma bayanan sirri na cewa 'yan kungiyar ISWAP ne suka kai harin.