SiyasaAfirka
Sojojin Najeriya sun musanta kai harin ramuwar gayya Delta
March 18, 2024![Wani atisayen sojin Najeriya](https://static.dw.com/image/66530590_800.webp)
Talla
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa sojojin Najeriya na ci gaba da kona dukkan gidaje da sauran gine-ginen da ke yankin tun bayan da wasu fusatattun matasa suka hallaka sojojin kasar kimanin 16 a karshen mako, wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin tun bayan barkewar rikicin kabilanci da kuma na mallakar kasa a yankin Okuoma da ke jihar Delta.
Karin bayani: Martani mai zafi kan kisan sojoji a Delta
Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya musanta kai harin ramuwar gayya yankin, inda ya shaida wa Reuters cewa kokarin bankado wadanda suka gudanar da aika-aikar suke ba wai maida martani ba.