1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Nijar sun zargi Faransa da shirya kai musu hari

September 10, 2023

Sojojin na Nijar dai sun sha nanata cewa za su kare kasarsu idan har aka yi yunkurin kai musu hari. Sai dai ba su fadi haka ba a wannan sanarwa da suka fitar a ranar Asabar.

Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Shugabannin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar sun zargi Faransa da fara jibge makaman yaki a kasashen da ke makwabtaka da Nijar domin ci gaba da shirya yadda Faransan za ta afko musu. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin Nijar Kanal Amadou Abdramane ya fitar ya ce tuni Faransa ta jibge jiragen yaki na soji da motoci masu sulke wajen 40 a kasashen Cote d'Ivoire da Benin.

Kanal Abdramane ya ce wadannan kasashe da ke cikin kungiyar ECOWAS ne ke bai wa Faransa damar murmurar karfin da za ta afka wa Nijar bisa sahalewar ECOWAS.

Dangataka tsakanin Faransa da Nijar ta yi tsami bayan da mahukuntan birnin Paris suka ce ba su amince da wata gwamnati a Nijar ba idan ba gwamnatin Shugaba Bazoum Mohamed ba ce da 'yan Nijar suka zaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani