Sojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100
February 22, 2020![Niamey Nigeria](https://static.dw.com/image/49373010_800.webp)
Talla
Ma'aikatar harkokin tsaron Jamhuriyar ta Nijar, ta ce baya ga kisan 'yan bindigar, mayakan sun kwace wata naurar hada bama-bamai.
Hukumomin sun ce babu asarar rai daga bangaren sojin kasar da ma na Faransar, tare da yaba nasarar da suka samu ta hanyar hada karfin.
Dama dai an karfafa tsaro a yankin na Tillaberi, tare da dakatar da amfini da babura, bayan hare-haren watan Disambar bara, da suka yi sanadiyyar mutuwar sojin kasar 174.
Akwai ma dokar ta-baci da ke ci a yankin yau shekaru biyu ke nan.
Kasar Faransa ta yi alkawarin kara yawan dakarunta a bana, a tsakanin wasu kasashen yammacin Afirka da ke fama da fitintinu, da kimanin 600 kan wasu dubu 4,500 da dama ke baje a kasashen.