Sojin Pakistan sun kai hari sansanin yan Alqaida
January 16, 2007Sojojin Pakistan sun sanar da cewar sun lalata wurare uku da ake zaton maboyar mayakan kungiyar al-Qaeda ne.
An dai sami nasarar hakan ne bayan kai wasu hare-haren bom a kusa da iyakar kasar da Afghanistan, inda har suka kashe mutane da daman gaske.
Wani kakakin rundunar sojan ta Pakistan yace jiragen saman yakin kasar sun kai hare-haren ne a kudancin lardin Waziristan, bayan da aka sami labarin cewar mayakan kungiyar al-Qaeda talatin sun buya a wannan yanki.
Kakakin na soja, Manjo-janar Shaukat Sultan yace wasu daga cikin wadanda aka kashe yan kasashen ketare ne, ko da shike ba’a san yawan su ba.
A watan Satumba na bara, gwamnatin Pakistan ta cimma yarjejeniya da shugabannin kalibun yankunan kasar, a game da farautar yan tarzoma na al-Qaeda a yankunan su.