Sojin Siriya sun soma yakin kwato yankunan kasar
October 8, 2015Sojojin Siriya sun kaddamar a jiya Laraba da wani gagarimin hari ta kasa a wani yinkuri na neman kwato yankuna kasar da ke a hannun kungiyar 'yan tawaye dama Kungiyar IS. Sojojin gwamnatin ta Bashar al-Assad wadanda ke samun dafawar jiragen sama dama na ruwa na yaki na kasar Rasha na da burin a halin yanzu kwato babbar hanyar da hada birnin Damas da na Alep na arewacin kasar.
Shugaban Rasha Vladmir Poutine ya bada sanarwar cewa za su ci gaba da kai hare-haren da suka soma kaddamarwa a kasar ta Siriya inda a cewar ministan tsaron kasar ta Rasha Serguei Choigou a cikin mako daya, jiragen yakinsu sun kai hari a kan gurare 112 na mayakan Kungiyar ta IS a kasar ta Siriya.
Sai dai a jiya Laraba Amirka ta zargi kasar ta Rasha da fakewa da wannan dama domin kaddamar da wadannan hare-hare nata a kan mayakan 'yan tawayen kasar ta Siriya masu saussaucin ra'ayi da ke da burin kifar da gwamnatin Al-Assad.