SiyasaAfirka
Sojin Sudan:Babu sulhu da RSF a cikin Ramadan sai sun fice
March 10, 2024Talla
Rundunar sojin Sudan ta ce babu batun amincewa da tsagaita wutar yaki a cikin watan Ramadan har sai dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo sun fice daga gidaje da yankunan fararen hula.
Karin bayani:Amurka ta koka da matakin sojin Sudan na hana shigar da agaji Darfur
Wannan dai sako ne da wani jigo a cikin rundunar sojin kasar da ke biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhan ya wallafa a dandalin Telegram a Lahadin nan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Karin bayani:Al'umma na fuskantar matsalar karancin abinci a Sudan
Tun a cikin watan Afirilun bara ne rikicin ya barke, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, musamman ma a yankin Darfur da kuma Khartoum babban birnin kasar.