Sojoji 5 na FINUL sun mutu a Libanon.
June 24, 2007Sojoji 5 na rundunar ƙasa da ƙasa ta Finul ,su ka rasa rayuka, wasu kuma karin 3 su ka ji mummunan raunuka a sakamakon fashewar wata bam a kudancin Libanon.
Rahotanin sun nunar da cewa, dukkan sojojin yan asulin ƙasar Spain ne.
kakakin rundunar ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da ke gudanar da ayyukan tsaro a Libanon, ya tabbatar da wannan alƙalluma,sannan Milöos Strugar ya ce, sun tura tawagar ƙurraru domin ƙarin haske a game da faruwar al´ammrin.
Majalisar Ɗinkin Dunia,ta tura runduna a ƙasar Libanon, domin kulla da yarjejniyar da a ka cimma, tsakanin Isra´ila da mayaƙan Hizbullahi na ƙasar Libanon, bayan yaƙin da su ka gwabza a shekara ta 2006.
A wani labarin kuma, da ya shafi Libanon ana ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin sojojin Gwamnati da dakarun ƙungiyar Fatah Al Islam.