1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya biyu za su fuskanci tuhuma

Suleiman Babayo MAB
May 2, 2024

Sojojin Najeriya biyu za su fuskanci tuhuma a kotun musamman ta soja kan harin da ya halaka mutane 85 a jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Harin Tudun Biri a Kaduna da ke Najeriya
Harin Tudun Biri a Kaduna da ke NajeriyaHoto: AP

A Najeriya sojoji biyu za su fuskanci tuhuma karkashin kotun soja, kan hari ta sama bisa kuskure da ya halaka mutane 85. A wannan Alhamis rundunar sojan kasar ta bayyana haka, shi dai harin kan kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ya faru ne a watan Disamba na shekarar da ta gabata ta 2023, lokacin da mazauna kauyen suke wani biki na addinin Islama na Maulidi.

Karin Bayani: An binne gawa 85 a kauyen Tudun Biri

Sanarwar ta ce bayan gudanar da duk binciken da ya dace an dauki matakin kan sojojin biyu da suka yi abin da za su fuskanci sharia.

Tun farko hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da binciken da ya dace, domin daukan duk matakan da suka mataka wajen kare gaba. Tun daga shekara ta 2017 sau hudu ana samun hare-haren ta sama bisa kuskure da suke ritsawa da fararen hula a Najeriya, kasa mafi yawan mutane tsakanin kasashen nahiyar Afirka, wadda take fusknatar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai.