Sojoji Iraki na samun galaba a Mosul
March 7, 2017Talla
Kakakin rundunar da ke fagen daga Leutenan kanal Abdel Amir al-Mohammadawi, ya sheda wa manema labarai cewa an dau tsawon sa'a guda ana luguden wuta da mayakan, kafin daga bisani suka samu galaba a kansu. Wannan ya basu nasarar kwace babban bankin kasar da kuma babban gidan tarihin birnin da ke hannun 'yan Kungiyar ta IS. A cewar rundunar sojin, kwace wadannan gine-gine, na zama wata dama da zai taimaka su kara nausawa cikin tungar IS da nufin tabbatar kwace cikakken iko. A tun shekara ta 2014 mayakan IS masu tsatsauran kishi addini suka karbe iko da birnin Mosul.