Sojoji na yin bore a Papua New Guinea
January 26, 2012Ratotannin daga Papua New Guinea na cewar wani habsan soja ya tabatar da karɓe ragamar rundunar sojojin ƙasar ;tare da jingine majalisar dokokin da kuma mayar da tsohon fraministan da aka sauke daga mulki Michael Somare a matsayin sa.
Habsan kanal Yaura Sasa mai ritaya wanda ya yi iƙirararin kan sa a matsayin shugaban askarawan ƙasar a Port Moresby babban birnin ƙasar ,a wani taron manema labarai da yayi ,ya ce ba juyin mulki ba ne ya yi, amma ya na buƙatar shugaban ƙassar Peter o -Neil ;ya sake mayar da fraministan akan aikin sa ,ya ce idan kuma bai yi haka ba ;to kam zai ɗau matakan da suka cancanta domin ceton dimokaradiyya.Tsohon fraministan Michael Somare mai shekaru 75 da haifuwa an sauke shi ne daga matsayin a tsakiyar shekara bara a lokacin da ya kai wata ziyara a Singapur domin yin jiya.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu