Sojoji sun cafke wasu 'yan Kungiyar Hizbullahi a Kano
May 30, 2013Jami'ai na rundunar sojin Najeriya sun ce mutanen nan da aka kama a Kano da tarin makamai a jiya na da alaka da kungiyar nan ta Hizbullahi da ke Lebanon wadda ta yi kaurin suna wajen gwagwarmaya da makamai.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya a garin na Kano Kaptain Ikedichi Iweha na cewar, tuni guda daga cikin mutanen wanda kwarori ne ya ce shi mamba ne na kungiyar ta Hezbollah.
Yanzu haka dai rundunar sojan Najeriyar ta ce ta shiga bincike wajen gano ko ya Allah mutanen da aka kama na da nasaba da tashe-tashen hankulan da ake alakantawa da Boko Haram a arewacin Najeriya.
A ranar Talatar da ta gabata ce dai sojoji su ka yi wa wani gidan kwarorin tsinke a unguwar masu hannu da shuni ta Bompai, inda su ka gano tarin makamai da su ka hada da gurneti da bindigogi da bama-bamai da albarusai da kuma irin rokokin nan na harbo jiragen sama.
Mawallafi: Ahmad Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madiobi