1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gomman mutane sun mutu a harin Ethiopiya

Zainab Mohammed Abubakar
June 24, 2021

Rundunar sojin Ethiopiya ta tabbatar da daukar alhakin mummunan harin da ya ritsa da wata kasuwa a lardin Tigray mai fama da rikici, harin da ya kashe sama da mutum 50.

Äthiopien Luftangriff Tigray-Region
Hoto: Tigray Guardians 24/REUTERS

Mai magana da yawun rundunar sojin, Kanar Getnet Adane, ya fada wa taron manema labaru cewar, an yi niyyar kai wa 'yan tawaye hari ne amma amma ba fararen hula ba, sabanin yadda ake yayatawa.

Ya kara da cewar, somamen da suka kai a garin Togoga na da nufin tarwatsa mayakan da ke mubayi'a ga hambararriyar jam'iyyar da ke mulki a Tigray, tare da gargadin cewar mayakan na fakewa ne da fararen hula.

Rahotanni na nuni da cewar akwai gomman mutane da ke kwance a asibitoci, wadansunsu sun rasa bangarorin jikinsu, a yayin da wasu ke jinyar munanan raunukan kuna, biyo bayan harin da rahotanni ke nuni da cewar yayi sanadiyyar rayukan sama da mutane 50.