Sojoji sun hambarar da gwamnati a Guinea-Bissau
November 26, 2025
Sojoji sun kifar da mulki a kasar Guinea-Bissau, tare da bayyana dakatar da duk wasu harkoki na zaben da kuma rufe iyakokin kasa, a yayin wata sanarwar da suka karanta a shelkwatar jami'an tsaro ta kasar.
Guinea-Bissau Shugaba Embalo ya ki sauka daga mulki
Da sanyin wannan Laraba, wasu bayyanai daga babban birnin Bissau, suka tabbatar da cewa dakarun sojan kundun bala, sun mamaye manyan hanyoyin da ke zuwa fadar shugaban kasa, inda aka yi ta jin harbe-harbe da manyan bindigogi a kusa da fadar shugaban kasa, lamarin da ya sa daruruwan mutane suka tsere domin tsira da rayukansu, sai dai har ya zuwa wannan lokaci, ba a san halin da shugaban kasar Umaro Sissoco Embaló yake ciki ba. Duk wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake jiran sakamakon zaben shugaban kasa da na ’yan majalisa da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Embalo ya kori firaminista Rui Duarte Barros,a Guinea-Bissau
A yammacin Talatar da ta wuce bangaren Embaló da kuma na babban abokin hamyyarsa, Fernando Dias de Costa, kowannensu ya yi ikirarin nasara, duk da cewa hukumomin zabe ba ta fitar da sakamakon wucin gadi ba tukuna.
Mata a Guinea-Bissau sun kona mahakar ma'adanai ta China
’Yan adawa sun yi zargin cewa an yi wata minakisa a zaben domin ba wa Mista Embaló damar ci gaba da mulki. Ita dai Guinea-Bissau na daga cikin kasashe mafi raunin tattalin arziki na duniya, inda fiye da kashi 40 cikin 100 na 'yan kasar na rayuwa a kasa da layin talauci.