Sojoji sun kame shugaban Mali
August 18, 2020Talla
Dakarun masu bore a Mali, sun kame Shugaba Ibrahim Boubacar Keita tare da Firaminista Boubou Cisse, wani daga cikin na gaba-gaba cikin dakarun masu boren ne ya sanar da hakan.
Kamar dai yadda rahotanni ke tabbatarwa, an kame shugabannin na Mali a gidan Shugaban kasa da ke a Bamako babban birni.
Tun da fari dai sojojin na Mali sun tayar da kayar baya ne a sansaninsu da ke garin Kati, 'yar tazara birnin na Bamako.
Wasu majiyoyi na sojin da ba su so a bayyana su ba, sun ce an mike da Shugaba Keita da Firaministan Cissen ne cikin wata tankar yaki a kan hanyar zuwa garin Katin inda sansanin sojoji yake.
Da ranar wannan Talatar ce dai dakarun na Mali, suka fara wannan boren da aka fassara da yunkurin kifar da gwamnati.