1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji na tarwatsa masu bore da karfi a Sudan

Abdul-raheem Hassan
June 3, 2019

Kungiyar likitoci a Sudan ta ce mutuane tara sun mutu wasu da dama sun jikata sakamakon amfani da karfin tuwo da sojojin suka yi wajen murkushe masu boren tabbatar da mulkin dimukaradiyya a kasar.

Sudan Soldaten in Khartum
Hoto: Getty Images/AFP/M. El-Shahed

Hukumomin mulkin soji a kasar Sudan sun tarwatsa zaman dirshan da masu fafutukar tabbatar da dimukaradiyya ke yi a gaban hedikwatar majalisar gudanarwar kasar.

Kungiyar kwararrun ma'aikata ta Sudan ta yi tir da matakin da sojojin ke dauka kan kungiyoyin masu zanga-zanga, tare da karfafa wa al'umma gwiwa na ci gaba da yi wa sojojin matsin lamba har sai sun mika mulki ga farar hula.

Tun a watan Disemban 2018 ne 'yan Sudan suka fara tada kayar baya kan tsadar rayuwa da kasar ke ciki, lamarin da ya kawo karshen mulkin tsohon Shugaban kasar Omar Hassan el-Bashir na tsawon shekaru 30 a watan Afirlun 2019.