Sojoji sun kashe masu hakar ma'adinai takwas a Ghana
January 20, 2025Akalla masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba takwas ne suka rasu sakamakon arangama da sojoji da ke gadin kamfanin hakar zinare na AngloGold Ashanti a tsakiyar yankin Obuasi na kasar Ghana.
A cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun bayyana cewa an yi artabu da mutanen ne a ranar Lahadi da dare kuma kusan 60 daga cikinsu na dauke da makamai da suka hada da bindigogi da arduna.
Hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Ghana
Sanarwar ta kara da cewa mahakan sun kutsa kai cikin shingen kamfanin da ke da lasisin hakar zinare ne a ranar Asabar da dare sannan suka bude wuta bayan motar sintirin soji ta korasu.
sojojin suka ce wannan shi ne ya sa suka mayar da martani domin kare kawunansu kuma ana cikin haka ne sai bakwai daga cikin masu hakar ma'adinan suka rasu.
Ghana da Mali za su yaki matsalar tsaro a kasashensu
Shugaban Ghana John Mahama ya bada umarnin bincike kan lamarin tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi tsakanin mahakan da kuma sojojin.