1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Mali

Abdul-raheem Hassan
June 16, 2019

Sojojin kawancen Faransa da na Mali sun kashe 'yan tawaye 20 a wani sumame da suka kaddamar a wani sansanin mayakan IS da ke arewacin kasar.

Mali | Soldaten am Flughafen von Mopti
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

Kakanin rundunar sojojin ya tabbatar da cewar ana ci gaba da bude wuta kan sansanin mayakan da ke iyaka da Nijar. Kasar Mali na fama da ayyukan ta'addanci tun bayan da 'yan tawaye  suka  mamaye yankin arewacin a shekara 2012,kafin daga bisani Faransa da sauran kawaye su sake kwato yanki.