1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji sun rufe offishin babbar jam'iyyar adawa a Yuganda

Zainab Mohammed Abubakar
July 22, 2024

Jami'an tsaro sun rufe hedikwatar babbar jam'iyyar ta NUP, a wani abin da mai magana da yawun 'yan sandan ya kira "matakin taka-tsan-tsan" gabanin zanga-zangar adawa da gwamnati.

Hoto: Hajarah Nalwadda/AP/picture alliance

A wani sako da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, shugaban jam'iyyar National Unity Platform Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine, ya ce jami'an tsaro sun kewaye hedkwatar jam'iyyar NUP da ke Kampala babban birnin kasar, tare da hana kowa shiga ko fita.

Ya ce an kama wasu shugabannin jam'iyyar ta NUP da yawa tare da nuna hotunan jami'an soji a harabar tare da wasu motocinsu da aka ajiye.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Kituuma Rusoke bai amsa kai tsaye ba lokacin da aka nemi jin ta bakinsa game da kamen shugabannin adawar.