1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun sake kashe fara hula a Siriya

November 4, 2011

Babu alamun kawo ƙarshen zubar da jini a ƙasar Siriya du kuwa da yarjejeniyar da gwamnatin Bashar Al-Assad ta cimma wa da ƙungiyar ƙasashen larabawa

Masu gudanar da zanga zanga a SiriyaHoto: picture alliance/dpa

Jamian tsaro a ƙasar Siriya sun kashe faran Hula guda 20 a garin Homs waɗanda suka buɗema wuta da bindigogi sa'ilin wata zanga zanga yayin da suka cfake wasu gomai a tsakiyar ƙasar.Wannan al'amari dai ya faru ne du kuwa da amince war da gwamnatin Bashar Al Assad ta yi da tayin ƙungiyar ƙasashen larabawa a taron ƙungiyar da ya gudana a ranar larba domin samun mafuta a rikicin siyasar da ya ƙiya ki canye wa.

Wanda gwamnatin ta Siriya ta amince ta janye sojojin ta daga cikin garuruwaN tare da sako yan adawar da ake tsare da su;tare da bada dama ga masu saka ido na ƙasashen duniya da kuma yan jaridu shiga ƙasar kafin soma tattauna ta neman sulhu tsakanin gwamnatin ta Siriya da yan adawar.ƙungiyoyin adawar dai ta hanyar shafin facebook sun yi kira ga magoya bayan su domin sake fitowa akan titunan a don gudanar da zanga zanga bayan sallah juma'a.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu