1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Sudan sun fara sako fararen hula

November 22, 2021

Sojojin Sudan sun sako farar hular da suka kame kafin juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata. Wannan na zuwa ne bayan amincewar da sojojin kasar suka yi na mika ragamar shugabancin Sudan din ga Abdallah Hamdok.

Sudan's Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

Shugaban jam'iyyar Congress Party Omar al-Degeir ya ce tun a yammacin Lahadi sojojin suka sako shi ya koma gidansa. Sauran wadanda aka sako din sun hada da 'yan siyasar jam'iyyar Umma Party da sauran wasu jami'ai.

Kasashen duniya sun yi maraba da mayar wa da Firaminista Hamdok mulkinsa bayan hambarar da shi da aka yi. Sai dai kuma Ministar Kula da Harkokin Kasashen Afirka ta Burtaniya Vicky Ford ta gargadi sojojin da lallai su martaba yarjejeniyar da aka kulla da su gabanin mika mulkin ga Hamdok.