1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sojoji sun yi musayar wuta a Somaliya

April 26, 2021

'Yan sanda a Somaliya, sun ce an yi musayar harbe-harbe a tsakanin sojoji a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na dorewa a kan mulki.

Somalia Gewalt zwischen Regierung und Opposition
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture alliance

Wasu rahotanni sun tababtar da cewa an samu bambancin ra'ayi ne a tsakanin dakarun kasar ta Somaliya, inda ake dora alhakin harbe-harben a kan sojojin da ra'ayoyinsu suka bambanta game da mulkin shugaban kasar, musamman a birnin Mogadishu.

Bayanai na cewa an yi ta jin karar harbe-harbe ne inda sojoji suka rufe galibin manyan hanyoyin birnin na Mogadishu.

A share guda, dandazon mutane ne suka yi ta maci suna nuna rashin jin dadinsu da ci gaba da zama a kan mulkin kasar da Shugaba Mohammad Abdullahi Farmajo ke yi, bayan karewar wa'adinsa cikin watan Fabrairu. 

Shugaban na Somaliya dai ya kara wa'adin nasa zuwa wasu shekaru biyu nan gaba.