1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen yunkurin juyin mulki a kasar Gabon

Zulaiha Abubakar
January 7, 2019

Bayan kira da a yi tawaye da wasu sojoji suka yi a Gabon, gwamnatin kasar ta ce ta shawo kan lamarin. Tun farko farko sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo yayin da shugaban ke jinya a Moroko.

Gabun mutmaßlicher Putschversuch des Militärs
Hoto: Radio Télévision Gabonaise - Screenshot

Bayan kira da a yi tawaye da wasu sojoji suka yi a kasar Gabon, gwamnatin ta ce kasar ta ce ta shawo kan lamarin. Tuni aka bayyana cafke daukacin sojojin da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin. Fadar gwamnatin kasar Gabon ta tabbatar mutuwar mutane biyu tare da kame wanda ya jagoranci yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bangosauran. Kawo yanzu dai gwamnati ta ce kura ta fara lafawa bayan da kasar ta shiga rudani.

Bayan shiga rudani da zullumin fargabar makomar kasar Gabon hannun soji, gwamnatin kasar ta ba da tabbacin kama Lieutenant Ondo Obiang Kelly jagoran sojojin da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Shuga Ali Bango, wata sanarwar fadar gwamnati na cewa an kuma kashe wasu sojoji biyu.

Shugaba Ali Bongo na kasar GabonHoto: Reuters/Reuters TV

Tun farko sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo wanda yanzu haka ake masa jinya a kasar Maroko. Sojojin sun kutsa cikin tashar yada labarun suka yi kira ga al'umma da su yi tawaye.

Rahotanni sun ce a wajen tashar wasu sojoji da ke wa shugaban biyayya sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa gungun mutane kimanin 300 da suka bazu kan tituna don nuna goyon bayansu ga yunkurin juyin mulkin.

Shugaba Ali Bongo ya gaji mahaifinsa Omar Bongo a shekarar 2009, amma ya lashe zaben shekarar 2016 a wani zabe da ake zargin an tafka magudi.