Rikon kwarya na shekaru uku a Burkina Faso
March 1, 2022Talla
An dai ba da wannan sanarwa ce a karshen wani taro na kasa da aka gudanar wanda ya hada sojoji da wakilai na kungiyoyin fara hula da sauran masu fada a ji na kasar. A cikin shirin dokar da aka cimma a taron wadda shugaban ya sa hannu a kai, ta tanadi cewar shugaban gwamnatin rikon kwarya Paul Henri Sandaogo ba zai tsaya takara ba a zaben shugaban kasa,ko na 'yan majalisa dokoki ko kuma na kansila a karshen wa#adin aikin gwamnatin wucin gadin.