Afghanistan na fuskantar barazanar tsaro
July 6, 2021Talla
'Yan taliban din sun karpe goman garurruan da ke a karkashin ikon gwamnatin abin da ya sa ake da fargaban faduwar gwamnatin ta Afghanistan. Yanzu haka Tajikistan ta tura sojoji sama da dubu 20 a kan iyakarta da Afghanistan yayin da Rasha ta rufe ofishin jakadancin a birnin Kabul. Masu aiko da rahotanin sun ce ficewar sojojin kawance na kasashen duniya daga Afghanistan ya kara dagula al'amuran tsaro a kasar.