Dakarun Amirka suna fita Afganistan
May 1, 2021Talla
Wasu bayanai na nuna cewa gwamnatin Amirka ta kashe kudi sama da dala tiriliyon biyu kan sojojinta da ke Afganistan, tun bayan da suka mamaye kasar a shekarar 2001 bayan aukuwar harin ta'addanci na ranar 9 ga watan satumba a Amirka.
Sai dai janye sojojin na zuwa ne a dai-dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu a sabon harin bam a masaukin baki da ke gabashin kasar ya karu zuwa 21, wasu 90 sun jikkata. Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin ko kuma harin yana da alaka da fara ficewar sojojin Amirka daga kasar.