Taimakon Amurka kan magance matsalolin tsaro?
February 17, 2026
Wata sanarwar rundunar tsaro kasar dai ta ce sojan na Amurka za su yi aikin horo da bada tallafi ga sojoji na kasar ne amma ba za su shiga cikin yakin na tsaro a ka tsaye ba. Can cikin batun takarda dai shigar Amurka cikin yakin na ta'adda na da babban burin kawo sauyi cikin annobar da ke neman komawa dashi mai rai guda tara.
To sai dai kuma sannu a hankali yaduwar ta Amurkawa zuwa sassa daban-daban na Najeriya na dauka ta hankali na 'yan kasar a halin yanzu.
Euraren da aka tura sojojin Amurka
Kama daga Maiduguri ya zuwa Kainji da ma Bauchi daga baya dai a cikin sunan horon dai Amurka tana kara fadada harkokin soja zuwa sassa daban-daban cikin arewacin kasar. Group Capt Usman Sulaiman dai wani tsohon jami'in sojan Najeriya ne da kuma ya ce ana bukatar kallon tsaf cikin rawa da kila takun na Amurka a yanzu.
A cikin sunan gayya ne dai sojan na Amurka ke tururuwa zuwa Najeriya a halin yanzu.
Sannu a hankali dai kara yawan na Amurka a cikin batun na yaki da ta'adda na nuna alamu na gazawa a bangaren tarayyar Najeriya da a baya tai suna wajen samar da zama na lafiya cikin kasashe na waje, amma kuma ke neman dauki yanzu.
Cece-kuce kan matakin
Duk da cewar dai ana kallon shiga ta sojan da idanu na tsaro, tuni da kara yawa da kila ma tasirinsu a sashen arewacin Najeriya ya fara zarcewa dauka ta hankali cikin kasar a halin yanzu.
Bauchi dai alal ga misali ba ta da tarihi cikin batun rashin tsaron da ke kasar yanzu haka. Kuma ko bayan nan daukacin yankunan guda uku dai na da albarkatun karkashin kasa. Da ma dai an dade Ana kallon rawar Amurkawan da idanun neman gindin zama a sashen arewacin da ke cike da ma'adinai iri-iri.