1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Sojojin Amurka sun kai hare-hare a Siriya

October 27, 2023

Sojojin Amurka sun kai jerin hare-hare a wasu sansanoni guda biyu dake zama tungar 'yan juyin juya halin Musulumcin Iran da kuma wasu kungiyoyi masu alaka da su.

Sojojin Amrka sun kai jerin hare-hare a SiriyaHoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

 

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an kai wadannan hare-haren ne bayan da shugaba Joe Biden ya gargadi jagoran Musulumci na kasar Iran Ayatullahi Ali Khamenei kan hare-haren da kugiyoyi masu alaka da su ke kai wa sojojin Washington da kuma barazanar fadada rikicin da ake tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila. Kazalika ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta kuma ce wadannan kungiyoyi sun kai wa sojojin Amurka dake Iraki da Siriya akalla hare-haren 16 a tsukin 'yan makwanni tare da yi ajalin ba'Amurke guda da kuma jikkata wadansu ma'aikata 21.

Tun farko dai jagoran musulumcin na Iran Ayatullahi Ali Khamenei ya zargi Amurka mai sojoji 900 a Siriya da kuma 2.500 a Iraki da jagorantar hare-haren da Isra'ila ke kai wa kungiyar Hamas a zirin Gaza inda ake ci gaba da samun asarar rayukan Falasdinawa.