Masu jihadi 10 sun halaka a Burkina Faso
May 29, 2020Dakarun kasar Burkina Faso sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 10 a yankin Worou da ke lardin Sourou a wani samame da suka kai wa 'yan ta'adda a sansaninsu na yankin yammacin kasar, shugaban sojojin na Barkina Fason ya sanar da hakan inda ya ce kwarya-kwaryar hadin gwuiwar dakarun da na 'yan sanda suka kai harin.
A 'yan kwanakin nan gwamnatin kasar ta matsa kaimi wajen fatattakar 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin na sahel.
Kasashen yankin da ke artabu da masu tada kayar bayan, sai dai batun karancin horo da kayan aiki shi ne ke kawo wa kasashen tarnaki a yakin da suke yi duk kuwa da gudunmuwar dakaru 5000 da kasar Faransa ta tallafa masu dasu.
Tun fara yakin a shekara ta 2015 akalla mutane 900 ne suka rasa rayukkansu yayin da 840,000 matsalar rashin tsaron ta raba su da muhallansu.