1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dakarun Chadi sun murkushe sabbin 'yan tawaye

April 19, 2021

Rundunar sojin kasar Chadi ta sanar a wannan Litinin cewa dakarunta sun hallaka 'yan tawaye 300 da suka kutso kai a arewacin kasar kwanaki takwas da suka gabata.

Nigeria Soldaten des Tschad patrouillieren in Monguno
Hoto: AFP/A. Marte

Sai dai ta ce a yayin gumurzun da aka yi a ranar Asabar sojojinta guda biyar sun rasa rayukansu. A ranar 11 ga watan Afrilun nan ne dai, ranar da ake zaben shugaban kasa a Chadi, gungun 'yan tawaye dauke da makamai masu hatsari ya shigo kasar daga kasar Libya. Tun daga lokacin ne kuma hankulan jama'ar kasar ke ci gaba da tashi. 

Mai magana da yawun rundunar sojin Chadi Azem Bermandoa Agouna ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, cewa artabun ya ba su damar kama 'yan tawaye 150. Gwamnatin Chadi dai ta ce a yanzu ta yi nasarar kakkabe 'yan tawaye a yankunan Tibesti da kuma Kanem.