Dakarun Ethiopiya sun kwace wani yanki
December 1, 2021Talla
Sanarwar na zuwa ne bayan nasarar da dakarun gwamnatin suka sanar da samu a yankin Amhara a karshen mako, na sake kwace Chifra da ke gundumar Afar, bayan da Framinista Abiy Ahmed ya bar babban birnin kasar Addis Ababa, domin shiga yaki kai tsaye a makon da ya gabata.
Nasarar mayakan gwamnatin dai, koma baya ne ga mayakan na Tigray da ke fatan isa birnin Addis Ababa da yaki ta cikin garin Amhara a kudanci, a ci gaba da yakin shekara guda na wannan kasa da yayi sanadiyyar dubban rayukan mutane tare da tilasta wasu miliyoyi kauracewa matsugunnensu.