1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi hayar sojoji daga Amurka

Jean-Fernand Koena | Mouhamadou Awal Balarabe Abdoulaye Mamane
December 30, 2023

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta tabbatar da kulla kawancen tsaro da sojojin hayan Bancroft na kasar Amurka da nufin horar da sojojinta.

Wasu sojojin ketare da ke aikin tabbatar da tsaro a guda daga cikin kasashen Afirka
Wasu sojojin ketare da ke aikin tabbatar da tsaro a guda daga cikin kasashen AfirkaHoto: French Army/AP/picture alliance

Sojojin haya na kungiyar Bancroft Global Development na Amurka sun riga sun isa Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da nufin sauke nauyin da gwamnatin kasar ta dora musu. Amma wannan mataki ya zo wa al'umma da mamaki, kasancewar ba sa dasawa da dakarun Wagner na Rasha da suka jima suna karyawa inda ba gaba a Afirka ta Tsakiya.

Saboda haka ne mutane da yawa suke fargabar barkewar rikici a nan gaba tsakanin sojojin na Rasha da takwarorinsu na Amurka, musamman don cin gajiyar arzikin ma'adinai da Allah ya hore wa kasar da kuma dalilan da siyasar kasa da kasa. 

Karin Bayani: Kamfanin tsaron Amurka na shirin shiga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Kakakin fadar shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Albert Mokpem Yaloké, da kansa ne ya kawo karshen damuwa da jita-jita da aka shafe kwanaki da dama ana yayatawa kan kasancewar sojojin haya na Amurka na Bancroft Global Development. Mokpem Yaloké ya ce Amurkawa sun zo kasar ne don horar da rundunar sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yana mai cewa.

“Amurka ma ta yi wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tayin horar da sojoji a nan gida da kuma a kasar Amurka. A tattaunawar da ke gudana tsakanin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da dukkan abokan huldarta, mu a kullun cewa muke, ba ma son irin wannan salo na aiki da ya tanadi cewa zan yi aiki da wannan amma ba ni aiki da wancan. A'a".

Babbaban jami'in fadar shugaban kasar Jamhuriyar Afirka, na hannunka mai sanda ne game da hadin gwiwa da za a yi tsakanin Amurkawa na kungiyar Bancroft da Rashawa na kungiyar Wagner. Sai dai wani mamba na gwamnatin kasar da ya nemi a sakaye sunansa, ya nuna damuwa game da yadda dangantaka za ta kasance tsakanin bangarorin biyu.

Wani sojan kungiyar tsaron Wagner ta Rasha a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Leger Kokpakpa/REUTERS

Ya ce duk da cewa bai tattauna wannan batu da abokin aikinsa da ke kula da harkokin waje ba, amma abin da ke kashe masa gwiwa shi ne yadda ma'amala za ta kasance tsakanin sojojin haya na Rasha, a kwamitin tsaron kasa da kuma Amurkawa, saboda yana ganin cewar zai haddasa rigima.

A bangaren kungiyoyin farar hula na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ma, akwai tsoron abin da ka je ya zo, sai dai Karl Blagué na kungiyar G16, ya yi imanin cewa ba zai yiwu a yi zaman cudeni-in-cudeka tsakanin sojojin Rasha da na Amurka ba.

"Ina fatan cewa an tsara hanyoyin da hankali zai kama na zuwan Amurkawa da za su horas da sojojinmu. Ba za a iya samun hadin kai tsakanin Amirkawa da sojojin haya na Wagner ba, musamman bisa la'akari da dukan cin zarafi da suka yi wa al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda suke da kwararran shaidu. Saboda haka, muna jiran shugaban kasa Faustin-Archange Touadéra, ya iya aiwatar da wannan tsari na shigowar da masu horaswa na Amurka."

Karin Bayani: Touadera na son inganta alaka da Faransa

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewar gwamnatin kasarta za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa da al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don cimma muradun hadin gwiwa domin samar da zaman lafiya da wadata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wacce za ta mutunta hakkin dan Adam tare da bin doka.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani