1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin haya Wagner na ficewa daga yankin Bakhmut na Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
May 25, 2023

Rasha ta maye gurbin sojojin hayan Wagner da dakarun kasar a yayin da shugaban kamfani Wagner ya sanar da fara janyewarsu daga yankin Bakhmut a cewar mataimakiyar ministan tsaron kasar Ukraine, Hana Maliar.

Russland Jewgeni Prigoschin Bachmut Wagner
Hoto: PRESS SERVICE OF "CONCORD"/REUTERS

A sanarwar ta Maliar, ta tabbatar da wannan sauyi, sai dai ta kara da cewar har yanzu sojojin Wagner na a cikin garin na Bakhmut yayin da dakarun Rasha ke tururuwar komawa.

Shugaban rundunar ta Wagner Yevgeny Prigozhin ya ce nan da farkon watan gobe na Yuni za su janye kwata-kwata daga yankin.

Mai magana da yawun dakarun sojin Ukraine da ke yanki gabashin kasar, Serhiy Cherevatyi ya ce a Rasha na kokarin sake takunta saboda mumunar asarar da suka janyo musu.

A satin da ya gabata ne Wagner ya sanar da karbe iko da garin na Bakhmut wanda suka kwashe tsawon lokaci ana gumurzu a kan shi.