1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Sojojin Indiya da Pakistan sun yi musayar wuta a Kashmir

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 8, 2025

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43, inda Pakistan ta rasa mutane 31 yayin da Indiya ta yi rashin mutane 12.

Jami'an tsaron India
Hoto: Basit Zargar/Middle east images/AFP/Getty Images

Dakarun sojin Indiya da Pakistan sun yi musayar wuta cikin dare a kan iyakar yankin Kashmir da kasashen biyu ke takaddamar mallakar ikonsa kusan shekaru tamanin kenan, kamar yadda rundunar sojin Indiya ta sanar a wannan Alhamis.

A ranar Laraba Indiya ta kai wasu munanan hare-haren makamai masu linzami zuwa makwabciyar ta ta, wanda ta ce ta tarwatsa tunga 9 ta 'yan ta'adda a Pakistan, makonni biyu bayan harin ta'addanci ya halaka 'yan kasar Indiya 26 a Kashmir da Indiyan ta zargi Pakistan da hannu, ko da yake Pakistan din ta musanta.

Karin bayani:Indiya da Pakistan sun yi musayar wuta

Ya zuwa yanzu rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43, inda Pakistan ta rasa mutane 31 yayin da Indiya ta yi rashin mutane 12, lamarin da ya sanya firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ikirarin cewa za su dauki fansar mutanen da Indiya ta kashe mu su.

Karin bayani:Rikicin India da Pakistan na yin kamari

Tuni dai kasashen duniya suka yi kira ga kasashen biyu su yi hakuri da juna su kwance damarar dakarunsu, cikinsu har da shugaban Amurka Donald Trump, inda ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ke shirin ganawa da takwaransa na Indiya a wannan Alhamis Subrahmanyam Jaishankar a birnin New Delhi, da nufin tausasa zukatansu, kwanaki biyu kenan bayan kai makamanciyar ziyarar zuwa Pakistan.