Sojojin Isra'ila sun ci gaba da luguden bamabamai kan Gaza
December 3, 2023Sojojin Isra'ila sun ci gaba da luguden bamabamai a Lahadin nan a yankin Zirin Gaza, a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da kiran sake kulla yarjejeniyar tsagaita wutar da ta kare a ranar juma'ar da ta gabata, domin dai kare fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Karin bayani:Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas ta kare ba tare da jin karin bayani ba
Hare-haren na Lahadin nan sun hallaka mutane 7, a yankin kudancin Gaza da ke da iyaka da Masar, sannan kuma suka far wa sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da tsakar daren jiya Asabar, tare da hallaka mutane 13, in ji jaridar WAFA ta Falasdinu.
Karin bayani:Gaza: Masar da Qatar na neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta
Babban likitan asibitin Al-Ahli Arab da ke Gaza Fadel Naim, ya ce a jiya Asabar kadai sun karbi gawarwaki 30, cikinsu har da kananan yara 7.