Sojojin Isra'ila za su dakatar da fada a wurare uku a Gaza
July 27, 2025
Sojojin Isra'ila sun fada a ranar Lahadi cewa za su dakatar da fada a yankuna uku na zirin Gaza a matsayin wani mataki na rage tsananin halin jin kai da ake ciki.
Sojojin sun ce za su dakatar da ayyuka a Muwasi da Deir al-Balah da kuma cikin birnin Gaza daga karfe 10:00 na safe zuwa 8:00 na dare agogon yankin a kowace rana har sai an bayar da wani sabon umarni.
Faransa za ta amince da Kasar Falasdinu
A cikin wata sanarwa, sojojin sun ce za su bayyana hanyoyin da za a bi domin taimaka wa kungiyoyin agaji wajen isar da abinci da sauran kayan tallafi ga jama'a a fadin Gaza.
Sojojin sun kuma ce ba sa fada a wadannan yankuna, amma an samu tashin hamkali da hare-hare a dukkansu a cikin 'yan makonnin nan da suka gabata.
'Yan majalisun dokokin Burtaniya 221 sun bukaci amincewa da kasar Falasdinu
A baya-bayan nan kasashen duniya sun rika sukar Isra'ila da ta bari a shigar da kayan agaji da abinci zirin Gaza saboda yadda yunwa ke kassara mutane ciki har da mata da yara kanana.