1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Jamus a Liberiya mai fama da cutar Ebola

Mohammad Nasiru AwalDecember 5, 2014

Ba dukkan ma'aikatan agajin da kasar ta Jamus ta tura yankuanan da ake fama da cutar Ebola suka je don son ransu ba.

Freiwillige für Kampf gegen Ebola
Hoto: Reuters/Bimmer

Bari mu fara da jaridar Der Tagesspiegel wadda ta mayar da hankali a kan ma'aikatan jinya da sojojin da Jamus ta tura kasar Liberiya don taimakawa a yakin da ake yi na kawar da cutar Ebola.

Jaridar ta rawaito wata majiya kwakkwara na cewa ba dukkan wadanda aka tura Liberiyar ne suka tafi don radin kai ba sabanin bayanan da mahukuntan Jamus suka yi. Daga cikin sojojin Jamus 50 da aka girke yankin Yammacin Afirka, 17 kadai a cikinsu suka je da son ransu. Sojojin za su taimaka wajen jigilar kayayyakin tallafi ta sama a kasashen da Ebola ta shafa. Ma'aikatar tsaron Jamus ta ce ba ta taba tunanin tura mutane gudanar da wannan aiki ba da son ransu ba. A cikin kwanaki masu zuwa wata tawaga da ta hada da likita guda ma'aikatan jinya shida za su tashi zuwa Monrobiya babban birnin kasar Liberiya don kula da lafiyar Jamusawan 'yan agaji da ke Liberiya don radin kai. A kuma halin da ake ciki wakilin majalisar dokokin Jamus a harkar tsaron kasa zai gudanar da bincike game da zargin na tura ma'aikatan agaji zuwa yankin na Ebola ba da son ransu ba.

Cin hanci da rashawa na kawo cikas ga yaki da ta'addanci

Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Cin hanci da rashawa tsakanin sojojin Kenya, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Tana mai cewa tun watanni da dama da suka wuce kasar ta Kenya da ke gabacin Afirka ke fama da hare-haren ta'addanci, amma hukumomin sun gaza shawo kan lamari.

Jaridar ta ci gaba da cewa a wannan makon ma ‘ya'yan kungiyar Al-Shabaab ta masu kaifin kishin addini sun sake hallaka ma'aikata 36 masu aikin farfasa duwatsu a arewacin Kenya. Hakan ya zo ne kwanaki kalilan bayan wani kisan gilla da 'yan tarzoman na Al-Shabaab suka yi wa fasinjojin wata safa inda suka kashe mutane 28. Jaridar ta ce hukumomin tsaron Kenya da ke fama da karancin kayan aiki da jami'ai kawo yanzu sun kasa magance ayyukan ta'addancin. Cin hancin da rashawa na kawo babban cikas ga yakin da tarzoma a Kenya. Kasar na daga cikin kasashen duniya da matsalar cin hanci ya yi wa katutu, kuma a dangane da ta'asar Al-Shabaab cin hancin da rashawar na barazana ga tsaron kasa.

Shugabancin Zimbabwe a hannun 'yan gidan Mugabe

Grace MugabeHoto: J. Njikizana/AFP/Getty Images

To daga batun ta'addanci da cin hanci da rashawa a Kenya sai maganar wanda zai gaji shugaban Zimbabwe Robert Mugabe. A labarin da ta buga game da babban taron jam'iyyar Zanu-PF jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce hankali ya karkata ga Grace Mugabe matar Robert Mugabe a taron na zaben sabon shugaban jam'iyyar. Jaridar ta ce yanzu dai Grace Mugabe mai shekaru 49 a duniya ta shiga cikin harkar siyasar kasar gadan-gadan, inda take samun cikakken goyon bayan mijinta. Ko shakka babu taron zai sake tabbatar da shugaba Mugabe a matsayin shugaban jam'iyyar sannan matarsa kuma a matsayin shugabar bangaren mata na jam'iyyar ta Zanu-PF, wanda haka zai tabbatar mata da wata kujera a shugabancin siyasa. Bisa ga dukkan alamu dai shugaba Mugabe ya share wa mai dakinsan fagen samun babban mukami watakila ma ta zama mataimakaiyarsa.