Sojojin Kungiyar AU da dama sun halaka a Somaliya
September 2, 2015Sojojin kasar Yuganda mambobin rundunar zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya ta Amison akalla 50 ne ake kyautata zaton sun halaka a kasar Somaliya a lokacin wani hari da mayakan Kungiyar Shebaab suka kaddama a cibiyar sojojin ta Jalane da ke a kudancin kasar a ranar Talatar Jiya.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wanda ya ruwaito wannan labari ya ce wata wasika da aka aika wa jami'an diplomasiyya a kasar ta Somaliya ne ta tabbatar da abkuwar lamarin inda ya ce mayakan kungiyar Shebaab din sun yi nasarar kwace barikin sojojin rundunar zaman lafiyar ta Amisom da ke a garin na Jalane kafin daga bisani sojojin kawancan sun sake karbeta a yammacin jiya Talata.
Kawo yanzu sojojin rundunar ta Amisom kimanin 100 ba a da labarinsu tun bayan abkuwar harin wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Somaliya.