1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji na son ECOWAS ta cire wa Mali takunkumi

September 22, 2020

Jagoran sojojin Mali da suka hambarar da gwamnatin farar hula a watan Agusta Kanar Assimi Goita ya bukaci shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da su janye tsauraran takunkuman da suka sanya wa kasar Mali.

Militärjunta in Mali ernennt Übergangs- und Vizepräsidenten
Hoto: ORTM TV/dpa/picture-alliance

A bayaninsa na wannan Talata Kanar Goita ya ce tun a jiya Litinin an nada shugaban gwamnatin riko kuma ya kamata kasashen na kungiyar ECOWAS su sakarwa kasar mara domin ta ci gaba da samun bunkasa.

Dama dai tun farko kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta lashi takobin ba za ta janye takunkumin da ta sanya wa kasar Mali ba har sai sojojin sun nada gwamnatin rikon kwarya wace farar hula zai jagoranta.