1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Mali sun haramta al'amuran siyasa a fadin kasar

April 11, 2024

Sakamakon kafa hujjar tabbatar da bin doka da oda, shugabannin mulkin Sojin Mali sun sanar da dakatar da dukkan al'amuran da suka shafi gudanar da taruka ko kuma gangami na siyasa har sai illah masha Allahu.

Shugaban kasar Mali Assimi Goita a wani rangadi a birnin Bamako
Shugaban kasar Mali Assimi Goita a wani rangadi a birnin BamakoHoto: Fatoma Coulibaly/REUTERS

Gwamnatin sojin Mali ta sanar da dokar haramta duk wani gangamin siyasa a fadin kasar, acewar mai magana da yawun sojojin Malin Abdoulaye Maiga a wata sanarwa da ya karanta ta kafar talabijin, inda ya kafa hujja da kudirin dokar sojin kasar da shugaba Kanal Assimi Goita ya rattaba hannu.

Karin bayani: Nijar: Sojoji sun ki cewa komai kan dage takunkumin ECOWAS

Matakin na shugaban mulkin sojin kasar Kanal Goita na zuwa ne a daidai lokacin da gamayyar jam'iyyun adawar kasar kimanin 80 suka rattaba hannu na hadin gwiwa wajen kalubalantar manufofin sojin a wata sanarwa hadin gwiwa da suka fitar a ranar 1 ga watan nan na Afrilu da muke ciki tare da bukatar dawo da kasar kan turbar dimukradiyya ba tare da bata lokaci ba.

Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojan Mali