1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Mali sun sake kwace birnin Kidal

October 7, 2026

Sojojin Mali sun kutsa Kidal ba tare da fuskantar turjiya daga 'yan tawayen Abzinawa ba, wadanda suka ce sun janye daga birnin saboda dabarun yaki.

Sojojin Mali FAMA a kan hanyar zuwa fagen daga
Sojojin Mali FAMA a kan hanyar zuwa fagen dagaHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Rundunar sojin Mali tare da tallafin sojojin hayan Rasha na Africa Corps, sun sake karbe iko da birnin Kidal da ke arewa maso gabashin kasar a ranar Talata.

Dakarun sun kutsa cikin Kidal ba tare da fuskantar turjiya daga kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta FLA da kawarta kungiyar JNIM mai alaka da Al-Qaida ba, wadanda birnin ke zama babbar tungarsu.

Wannan nasarar ta samu ne bayan da sojojin Mali suka kaddamar da gagarumin farmaki a yankin da nufin fatattakar kungiyoyin da suka kira 'yan ta'adda tare da dawo da harkokin gwamnati a birnin Kidal mai matukar muhimmanci.

Sai dai kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta FLA ta fidda wata sanarwa, inda ta ce ta janye daga Kidal ne a matsayin salo da dabarun yaki da kuma kiyaye hadarin da ka iya shafar fararen hula.

Yan awaren Azawad na Mali sun yi ikirarin kwace iko da Kidal

A cikin watan Afrilu da ya gabata ne dai 'yan tawayen FLA da kawayensu na JNIM suka kori sojojin Mali daga Kidal bayan gwabza kazamin fada, kuma sake kwace birnin na zuwa ne a daidai lokacin