1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun bude wasu hanyoyi a Maiduguri

Salissou BoukariFebruary 28, 2016

Bayan da suka shafe kusan shekaru uku suna rufe, bisa dalillan hare-haren 'yan Boko Haram sojojin Najeriya sun bude wasu mahimman hanyoyi a kewayen Maiduguri.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Manyan sojan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Daga cikin hanyoyin akwai wadda ta hada Maiduguri babban birnin Jihar Borno, da kuma Damboa da ke Kudu maso Yammaci. Sannan zuwa Mafa, Dikwa da kuma Gamboru Ngala da ke yankin gabashi duk sun kasance a halin yanzu ana iya zirga-zirga a kansu a cewar babban komandan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai.

Wata hanya ma da ke zuwa daga garin Damboa zuwa Biu inda aka yi ta fuskantar hare-haren 'yan kungiyar ita ma an bude ta. A halin yanzu dai, wata sabuwar bataliyar sojoji ce da aka girka a 'yan kwanakin nan, ke ci gaba da sintiri bisa babura domin kara tabbatar da cikekken tsaro a yankin kamar yadda babban jagoran sojojin kasar ya sanar.