1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya sun ceto daliban da aka sace a jihar Kogi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 7, 2026

An sace daliban a gidan marayu ranar 26 ga Afirilun 2026 a makarantar Daarul-Kitab da ke birnin Lokoja na jihar Kogi.

DW-Interview Nigeria | Verteidigungsminister Christopher Musa zur Sicherheitslage
Hoto: DW

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto dalibai bakwai da kuma mata biyu da 'yan bindiga suka sace, a wani gidan marayu na jihar Kogi da ke yankin arewa maso tsakiyar kasar.

Karin bayani: Yaushe za a samu tsaro a Bornon Najeriya?

Sanarwar da mataimakin daraktan yada labaran rundunar Laftar Hassan Abdullahi ya fitar ranar Laraba, ta ce daliban da ake kubutar, sun hada da maza biyar da mata biyu da kuma wasu manyan mata biyu, da ake kyautata zaton matan mai gidan marayun ne.

Karin bayani: An cika shekaru 12 da sace ‘yan matan makarantar Chibok

A ranar 26 ga Afirilun 2026 aka yi garkuwa da mutanen, daga makarantarsu ta Daarul-Kitab da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi, amma cikin hanzari aka sako 15 daga cikinsu, kafin 'yantar da ragowar a wannan karo.

Ko da yake har zuwa wannan lokaci babu wata kungiya da ta yi ikirarin sace daliban.