1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 79

January 25, 2025

Nasarar ta sojojin na zuwa ne yayin da dakarunsu suka matsa kaimi wajen ganin sun kamo rikakken dan bindiga Bello Turji, inda tuni sojojin suka yi nasarar kashe mataimakinsa Aminu Kanawa a 'yan kwanakin da suka gabata.

Nigeria Major General Olufemi Olatubosun Oluyede
Hoto: Ubale Musa/DW

Rundunar sojin Najeriya ta hallaka 'yan bindiga kusan 80 a cikin makon da ya gabata. ta sanar da haka ne a ranar Jumu'a, inda mai magana da yawunta Manjo Janar Edward Buba ya fitar da sanarwa yana mai cewa sabon samame da dakarunsu suka kadamar a sassan Najeriya dabam-dabam ya kai ga kama mutum 252 wadanda ake zargi da aikata munanan laifukada kuma kubutar da mutum 67 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Hira da Janar Christopher Musa

06:48

This browser does not support the video element.

Cikin mutanen da aka kama akwai guda 28 da ake zargi da kwarewa wajen satar danyan man fetur a kudancin kasar, wanda ya dauki dogon lokaci yana haddasa wa Najeriya babbar asara a kudaden shigar da take samu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW