Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau
September 25, 2014![Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv](https://static.dw.com/image/17631055_800.webp)
Talla
Rundunar ta sanar da cewar sojojin sun samun gawar mutumin da ke zama jagoran masu tada kayar bayan.Kakakin sojin Najeriyar Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa manema labarai a birnin Abuja cewar,an kashe Mohammed Bashir yayin fafatawar da aka yi a garin Konduga na Jihar Borno,da ke a yanki arewa maso gabashin ƙasar.
Kuma shi ne yake fitowa a faifan bidiyo a matsayin jagoran ƙungiyar, wato Abubakar Shekau wanda aka daɗe da kashewa.Mun tanadi rahotanni na bita dangane da irin wahalolin da Boko Haran ta janyo wa Najeriya.