1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Nijar sun kashe jagoran Boko Haram na tafkin Chadi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 22, 2025

Kafin kashe shi, sai da ya jagoranci kai munanan hare-hare a kasashen Najeriya Nijar Chadi da kuma Kamaru, wadanda suke da iyakoki da juna.

Tawagar sojojin Nijar a yankin Bosso na jihar Diffa
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da halaka jagoran kungiyar ta'addanci ta Boko Haram na kasashen yankin tafkin Chadi, mai suna Bakura, bayan wani samame da ta kai garin Diffa da ke kudancin Nijar.

Sanarwar da rundunar ta fitar ranar Alhamis, ta ce tun asali Bakura yana biyayya ga tsagin shugabancin Abubakar Shekau na Boko Haram, wanda yake tsananin gaba da kungiyar ta'addanci ta ISWAP.

Kafin kashe shi, sai da ya jagoranci kai munanan hare-hare a kasashen Najeriya Nijar Chadi da kuma Kamaru, wadanda suke da iyakoki da juna.

Karin bayani;Yan ta'addan IS sun halaka manoma 15 a Arewacin Najeriya

Daga fara ayyukan ta'addancin Boko Haram a shekarar 2009 zuwa yanzu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun janyo asarar rayukan mutane dubu arba'in, tare da raba sama da miliyan biyu da gidajensu.