1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram a yankin Diffa

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2024

Wani fada da aka gwabza a yanin Kudu maso Gabashin Nijar ya yi sanadin jikkatar sojoji 10 tare da kashe mayakan da dama, a cewar sanarwar ma'aikatar tsaron Nijar.

Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A wannan Talatar (23.01.2024) ce mayakan Kungiyar Boko Haram suka kai hari kan wata rundunar shiga tsakani ta musamman, da ke filin jirgin saman N'Guigmi, wani gari da ke yankin Diffa a kusa da kan iyaka da Najeriya.

Fadan wanda aka fara da misalin karfe biyun dare ya dauki kimanin mintuna 20 kafin a fatattaki maharan zuwa gabar tafkin Chadi, kamar yadda ma'aikatar ta shaidar.

Tafkin na Chadi dai ya ratsa iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, inda tsawon lokaci mayakan na Boko Haram ke amfani da shi wajen afka wa mazauna kan iyakokin kasashen.