1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100

Abdoulaye Mamane Amadou
July 4, 2024

A matsayin martani kan mummunan harin da 'yan ta'adda da ya kashe sojanta 20, rundunar sojan Nijar ta yi ikrarin kashe 'yan ta'adda fiye da 100 a yayin samamen da ta kai a yankin Tillaberi

Rundunar sojan Nijar mai yaki da ta'addanci
Rundunar sojan Nijar mai yaki da ta'addanciHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Sojojin Nijar sun tabbatar da kisan 'yan ta'adda fiye da 100 a samamen da suka kai ta sama da kasa kan mabuyar 'yan ta'adda a yankunan da ke iya dar kasar da Burkina Faso.

Karin bayani :Nijar: Bukatar sakar wa 'yan siyasa mara

Rundunar tsaron Nijar ta ce ta kashe mayakan ne a matsayin martani kan mummunan harin ta'addanci da masu da'awar jihadi suka kai a makon da ya gabata tare da kisan sojoji 20 a yankin Tassia na yammacin kasar.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce ta kuma halaka wasu karin 'yan ta'adda takwas tare da kama wasu 19 a samamen da takai kan kasuwannin yankunan Dougouro da Bankilaré da ke iyaka da Burkina Faso.

Karin bayani : Harin ta'addanci a kasar Mali ya hallaka mutane 40

Kungiyoyin masu ikrarin jihadi dai na ci gaba da cin karensu ba babbaka a yankunan Tillaberi na yammacin Nijar mai iyaka da kasashen Mali da Burkia Faso tare da halaka dumbin fararen hula.