1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Sudan na kara samun galaba a kan dakarun RSF

Binta Aliyu Zurmi
February 6, 2025

Sojojin gwamnati a Sudan sun kaddamar da wani sabon farmaki a kokarinsu na mayar da yankunan birnin Khartoum karkashin ikonsu.

Sudan | Soldaten der sudanesischen Armee feiern ihren Einmarsch in Wad Madani
Hoto: El Tayeb Siddig/REUTER

A cewar sanarwa da suka fidda bayan kwashe makwanni ana gumurzu sun kwace wasu yankunan da dama na birnin daga hannun sojojin RSF.

Wata majiya ta sojojin gwamntin ta ce dakarun Sudan na kara tunkarar yankunan da sojojin Mohammed Hamdan Daglo suka kafa shinge.

Ko a makon da ya gabata shugaban sojojin sa kai na RSF ya bayyana irin koma bayan da suke samu a yakin da suke gwabzawa da sojojin gwamnati.

Rikicin shugabanci da ya barke a tsakanin bangarorin biyu tun a watan Afrilun 2023 ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar salwantan rayukan dubban fararen hula tare da raba wasunsu da matsugunansu.

 

Karin Bayani: Yan tawayen RSF a Sudan sun kashe akalla mutum 60 a Omdurman